Friday, January 18, 2008

Matasa

Hakika, Matasa su ne makomar kowace al'umma, Hausa Fulani na da matasa masu hazaka a dukkan fannoni na ilimi. Ganin haka ya sa TSANGARWA FOUNDATION ta ga dacewar samar da wannan Dandalin da nufin bawa matasa damar haduwa waje guda don amfanar da juna.Ko shakka babu, 'biyu ta fi daya ko a rabon dauki' in ji malam Bahaushe. Saboda haka muna ga lokaci ya yi da matasa za mu zabura mu zage dantse wajen haduwa waje guda don bawa al'ummarmu gudunmawa ta hanyar yada Abubuwan da suka shafi ilmin Kwamfiyuta da Hausa don amfanin al'ummarmu wadanda ba su samu nasarar yin karatu mai zurfi ba koma sam-sam ba su yi ba a fannin boko don suma su ci gajiyar wannan Fasaha da a yanzu tauraruwarta ke haskakawa a duniya.Muna sauraron mukalolinku don dubawa da gyarawa tare kuma da aikawa duniya.
Godiya daga Mustapha Daham Dala.

No comments: