Friday, January 18, 2008

Auren Danja Da Mansura

wanda angon ya biya lakadan ba ajalan ba. Da yake jawabi jim kadan bayan daura auren, Malam Ahmed Usman, wato Limamin Masallacin, wanda kuma shi ya daura auren, ya ja hankalin ma'auratan da su ji tsoron Allah a al'amurransu. Inda ya ce, “Sani da Mansura duk fitattun yara ne masu hazaka. Don haka su yi amfani da wannan hazaka wajen taimakon addinin Musulunci.”

To tun kafin a daura auren, an gudanar da shagulgula daban daban. Biki dai ya yi kyau, ya tsaru, ya kuma ba kowa sha'awa. Domin ko da 'yar shugaban kasa da dan shugaban kasa ne, iyakar bidi'ar da za a yi kenan. Anko kala bakwai aka ba mutane saba'in kyauta. An fara bikin ne da kamu a ranar takwas ga wata. Goma ga wata kuwa, aka yi Cultural Nite, yayin da sha daya ga wata aka yi yinin biki da rana, da daddare kuma aka yi Arabian Nite.

Ranar sha biyu ga wata, da yake ango da amarya duk yarbawa ne, ranar ce aka gudanar da 'Yoruba Nite'. Kai amarya kuwa, an yi shi ne ranar da aka daura aure, wato sha hudu ga wata. Washegari sha biyar ga wata kuwa, ranar ce aka yi Dinner , inda ango da amarya suka nuna lallai su ba Hausawa bane. Domin kayan da suka sanya irin kayan da Kiristoci ke aure ne a Coci da su. Af, na manta da Engagement Evening, ran da aka yi Fareti. Ango da abokansa sun sha zarya.

Nan ne bisa ga al'adar Yarbawa ake gwada ango ko zai iya hakuri da matarsa. Ko da yake da Yarbanci aka yi ta yin maganganun, amma abinda ya ba kowa dariya, sai aka zo da wani dan Bunsuru ya sha wani abu a wuya kamar Neck Tie, da Doya da Man Ja, da buhun Gishiri, aka dosa sanya Sani Danja Fareti, ya je ya dawo. Ita kuwa Mansura tana hakince. Bayan da aka lura ya jigata ne, sai aka ce ya zo ya tsugunna gabanta. Aka tambaye shi, “Because of what ka zo nan?” Sai ya ce “Because of Marriage”. Sai aka ce a'a, ya ce Because of Mansura. Ya ce “E, Because of Mansura”.

Daga nan sai aka barke da Yarbanci. Da yake wakilinmu ba ya jin Yarbancin, sai ya tambayi wani a wajen, “Wannan gwalagwalam da Sani Danja yake yi a gaban Mansura me yake cewa?” Shine aka ce mashi wai alkawari ya dauka cewa shi da Mansura mutu ka raba, babu kishiya. Sannan kuma dan Bunsuru mai Neck Tie da sauran kayayyakin abinci, iyayen Sani suka kawo, inda suke nuna lallai cewa dansu zai iya ciyar da matarsa.

Jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da wannan biki. To amma magana ta gaskiya, wadanda suke Allah wadai sun fi wadanda suke cewa Allah ya sanya albarka yawa. Kowa ka tambaye shi yana da nashi dalilin. Amma ma fi yawan jama'a ba su ji dadin yaudarar Maryam Jankunne da Sanin ya yi ba, shi yasa suke Allah wadai da bikin. Wasu kuma suna ganin kamar Mansura ba ajin Sani ba ce. Don haka ba su ji dadi ba.

Wata kuma cikin bacin rai, tuna irin kurin da Sanin ya yi ne a wakarsa, inda yake cewa shine mai buhu-buhun 'yan mata kalakala, da kuma inda yake cewa “Ni sai na darje, don kar in yi zaben tumun dare.” To shine take cewa “Duk cikin buhu buhun 'yanmatanshi, ya rasa wadda zai zaba sai Mansura? To me ya gani? Diri? Ko asali? Ko ilimi? Ko kudi? Ko kuma kamun kai?” Don jin dalilin da yasa ya zabi Mansura daga cikin buhu buhun 'yanmatanshi, shine wakilin mu ya tambaye shi ko me ya gani? Shi kuma sai ya ce, “Mansura mace ce mai addini, sannan kuma tana kaunata ainun. Ba kuma ni kadai ba, har dangina. Ga ta da biyayya da sanin ya kamata. Sannan kuma mace ce mai taimakawa iyayenta a ko da yaushe.”

To mai karatu ka ji dalilin da yasa Sani ya auri Mansura. To amma ita kuma fa, me ta gani game da angon na ta? Babbar mota ta gani koko Babbar Riga, ko Dalar da ya tara? Kuka ta barke da shi tana cewa “Na godewa Allah da ya nufe ni da ganin wannan muhimmiyar rana. Wai yau Sani Danja mijina ne na kaina ni kadai. Sannan kuma iyayena suna da rai, su suka ba da ni.” Ta yi kuma takaicin rabuwa da masoya finafinanta. Inda ta ba su hakuri. Mai karatu, ba ta amsa mana tambayarmu ba saboda rudewa. Don haka kai sai ka yanke hukunci.

Shi kuwa Ibrahim Musa, wato yayan ango cewa ya yi, Sani shine dan auta a cikin maza, kuma shi ya yi aure na karshe, inda ya ba shi shawara da cewa, tunda dai shi ya ga Mansura ya ce yana sonta, to wajibi ya yi hakuri da ita. Sannan kuma ya toshe kunne da maganganun jama'a. Ita kuwa Hafsatu Adike, wato uwa ga ango, godiya ta yi ga Allah, ta yi kuma farin ciki da kasancewa, duk da yake ya tashi a cikin Hausawa, amma sai ya auri Bayarbiya 'yar uwarsa, inda ta ce wannan ba karamin abin farin ciki bane. Don haka sai ta yi fatan wadanda suka zo bikin, za su koma gida lafiya.

Da take tofa albarkacin bakinta dangane da bikin, Malama Fati Musa, wadda kanwa ce ga angon cewa ta yi, ita ta goyi bayan wannan abu dari bisa dari. Sai ta yi fatan Allah dai ya saba halin ma'auratan, ta yadda mahassada za su ji kunya. Shi kuma da yake jawabi, Alh. Surajo Abdl-Wahab, wanda waliyi ne ga Mansura cewa ya yi, “Duk wani uba yana farin cikin ganin irin wannan rana. Ya kuma yaba da hankalin ma'auratan, inda suka yanke shawarar raya Sunnar Manzon Allah SAW. Sai dai ya tunatar da Sani cewa su fa mata a karkace suke, in ka ce za ka daidaita su, to za su karye. Don haka ya bi matarsa a hankali.

A halin da ake ciki dai, tuni amarya ta tare a dakinta. kila ma an samu rabo. Sai dai kash! Ba a samu zuwa Honey Moon Dubai ba. Wannan ya faru ne sabili da wai rashin samun Booking da ba su yi ba a satin da suka yi niyyar zuwa. An ce ko da Agent din ya sanar da Yakubu, nan take ya bugawa Mansura waya cewa babu zuwa Honey Moon, sai dai kila Umrah. Ko ma me kenan dai, an yi biki lafiya an kuma gama lafiya. A madadin Kamfanin Gidauniya, muna mika sakon taya murna, tare da fatan su duka za su ce gwamma da aka yi.

1 comment:

Unknown said...

Loved your site, Lee! Thanks for sharing Kami menyediakan berbagai macam obat seperti Obat kondiloma , Kencing Nanah , Wasir , Sipilis , Herpes , Diabetes