Friday, January 18, 2008

Hira Tsakanin Ibro

Shin wanene Ibro? Wai ya ma yi karatun boko kuwa? Matansa nawa? Ya yake ji game da mutuwar jarumansa guda biyu, wato Shu'aibu Kulu da kuma Yautai? Zai iya samun wadanda za su maye gurbinsu kuwa? Da gaske ne tun lokacin da suka rasu baya jin dadin wasa? Duk dan wasan ya amsa wadannan tambayoyin a cikin hirar da Gidauniya ta yi da shi kamar haka.
Sunana Rabilu Musa Danlasan, amma an fi sani na da Ibro.
Me yasa ake kiranka Ibro?
Asali sunan wani kakana ne, to ni kuma sai na yi amfani da shi wajen wasan kwaikwayo, daga nan sai sunan ya bi ni.
Ka bamu takaitaccen tarihinka
An haifeni a shekarar 1971. Na yi karatun Firamare dina a Danlasan da ke cikin karamar hukumar Warawa. Na kuma yi Sakandare na a Kwalejin horon malamai ta Wudil (Teachers College). Daga nan ne na shiga aikin gidan Yari (Prison Service) a shekarar 1991. Na yi shekara takwas ina aikin Gandiroba, daga nan na bari na cigaba da sana'ar wasan kwaikwayo.
Wane mukami ka rike a lokacin da kake aikin Gandiroban?
Na samu mukamin Insifeto kenan, sai kuma na bari.
Wace shekara ka fara wasan kwaikwayo?
Na fara tun ina aji uku a Sakandare. Kuma tun ina Firamare a kauyenmu, duk inda ka ga ana dariya to nine a wurin.
Kwanan nan 'yan wasanka guda biyu Allah ya yi masu rasuwa, watau Kulu da kuma Yautai, Allah ya jikansu. Masu kallon wasanninka sun zura ido su ga wata kila wasanninka sun ja baya, amma kafin nan, ya ka ji game da rashin wadannan jigajigan 'yan wasa naka?
Dama ai sabo ne yasa ake yiwa mutuwa kuka. Ko iyayensu haifarsu kawai suka yi, amma mu da muke tare muke morar juna, kuma mun shaku mun zama daya. Saboda haka mutuwar babu wanda zai ji ta kamar ni, kuma ni ke jin ta har gobe. Amma kar mutane su manta, ba wai su Kulu da Yautai sun rasu ba, ko Ibro ne ya rasu ba za a daina harkar wasan kwaikwayo ba. Saboda haka dama can ai Allah ne ya hada mu, kowa garinsu daban, ka zo na zo ne. Kuma har yanzu akwai mutanen da suke zuwa a sa su a finafinan mu. To amma dai na tabbatar ba za a taba samun kamar Kulu da Yautai din ba. Amma komai na Allah ne, shi ya hada mu, sai ka ga ya kawo wata hanyar.
Amma ni ina tabbatarwa mutane cewa in dai ta bangaren harkar mu ne, ni jiki na bai mutu ba. Inda kawai jikina ke mutuwa, sai dai idan na jeho wata maganar ina cikin wasa, nikan rasa wanda zai yi daidai da su din, amma gaba-gaba sai ka ga Allah ya kawo wani. Muma nan duk za mu tafi. Domin kafin a haife mu, akwai irin su Malam Mamman, duk sun yi ba a san mu ba, har muka zo muka taso aka san mu din. To saboda haka mu za mu ce daga kan mu abin ya tsaya ne? Ai ba zai yiwu ba. Mu ma za mu tafi wasu su taso, ko kuma muna da rai su taso. Ko kuma muna yi din a ce mu fito amma mu kasa yi. Ka ga dole wasu su zo su yi, kuma a yi sha'awarsu.
Kulu da Yautai, kafin rasuwarsu sun dan yi jinya. Ko hakan ta sa ka cire rai da su dama tun kafin su rasun, ko kaima rasuwar ta zo maka ne ba zato ba tsammani?
To ai kana da lafiyarka ma Allah ya kan dauki ranka. Saboda haka a nan in dai ta bangaren mutuwa ne ban yi mamaki ba. Kuma ba wai kamar yadda mutane suke rade radi ba, wannan ya ce abu kaza ne ya kashe Kulu, to Kulu abinda ya kashe shi, Basir ne aka yanke masa, daga nan ya samu matsala ta jini da ya yi ta zuba. Matsalar da ya samu kenan, har mutane suke kawo wasu cututtuka daban.
Shi kuma Yautai cutarsa ta wata irin Hajijiya ce, wanda idan yana zaune, idan Hajijiyar nan ta taso masa, idan kuna tare ma ba za ka san ta zo masa ba. Amma idan har ya mike tsaye, to zai fadi. To wannan itace cutar da ta kashe shi. A daina wani meye kaza-kaza.
Kana da iyali?
A to kuma ni na yau ne? Kowa ya kalle ni ai ya san ina da iyali.
Matanka nawa?
Matana uku, akwai Jamila, Kubra da Auta.
'Ya'yanka nawa?
Ina da yara takwas.
Ko za ka iya fada mana sunayensu?
Akwai Faisal, Jawahid, Lawiza, Abdul-Mummuni, Abbana, wato mai sunan babana. Sannan akwai Asma'u, Annabe, Sa'adiyya, Akwai wani yaro kuma da na Haifa na sa sunan mai gidana wato Baba Yaro.
Yanzu ka samu daukaka da rufin asiri, kuma duk inda ka tafi mutane na ga Ibro ga Ibro, ya kake ji akan hakan?
To mu dama mun riga mun saba. Kuma dama ko baka da ko Sisi, idan kana da jama'a, to sai ka godewa Allah. Waye ba zai yi masa dadi ba idan ya je wuri ya ji an kira shi, baka san mutum ba, ai dole ka ji dadi. Sai dai dama wasu suna fassara mu da mummunar kalma.
Kana kallon finafinan Indiya ko na Legas?
Ni gaskiya wannan baya gabana. Domin kuwa abinda ke gabanka shi za ka tsaya ka saurara. In ka duba, ko wakokin da nike yi, to nawa nike yi na gargajiya. Ba za ka taba ganin na canza wata waka ba ko kuma in yi wani abu daban, in dai can wani ne ya yi shi.
To amma ka yi Ibro Awilo, kuma ba wakar gargajiya bace.
Ina kai ka. Ai in ka kalli Ibro Awilo, ni cewa na yi a daina shan ganye. Ka ga kenan wa'azi na yi.
Ka goyi bayan a rika rawa da waka a finafinan hausa?
A'a, ni ban goyi baya ba. Amma waka tana da mafani idan tsarkakakkiya ce, haka rawa ma tana da amfani idan tsarkakakkiya ce.
To kai kana da gwani ko gwana a fagen finafinan hausa, wanda ke baka sha'awa, tunda ka ce baka kallon sauran finafinai sai na hausa?
Ina da Ciroki.
A mata fa?
Ina da mata wadanda a yanzu duk 'yan wasan mu na Hamdala ko kuma Ibro Films Production, duk 'yar wasan da ta fito in ta taka maka wasa kai ka san cewa ba karamar 'yar wasa bace, kuma ta zauna da gogaggun 'yan wasa.
Me yasa ba a yawan ganinka da Tsigai a finafinai karma da?
Ai ka san abubuwan ne da yawa. Misali, wasu na cewa an rabu da dai sauransu. To Tsigai dai muna tare da ita, amma sunan mu ne ya riga ya bazu a duniya. Yanzu sai ka ji can ana nemanka nan ana nemanka. To idan ba a rarrabu wasu sun je nan wasu sun je can ba, duk da haka ma wani wurin ana nemanmu, amma har mu gama rayuwarmu ba za mu je wajen ba.
Kana kallon Sentimental, wato finafinan da ba irin naku na ban dariya ba?
Har ka sa cikina ya yi ciwo. Ina haduwa da 'yan Sentimental din dai, amma bani kallo.
Me yasa?
Ai da Nigerian Film da Sentimental duk bani kallonsu.
To saboda me?
Ni dai kawai, ka san ra'ayi ne, Cin Danwake da Diga.
Me yasa kake yiwa 'yan Sentimental habaici a finafinanka?
Idan ka ji na tabo su, to na yi tsokana ne kawai. Kuma in kana tare da mutum ai dole ka dan rika tabo shi. Wani wasa ne, wani kuma da gaske ne.
Kamar Ali Nuhu, wasa kake yi masa yawanci koko?
Wasa ne.
Shi ma Yakubu Lere kana yawan tabo shi.
Wannan danmu ne, dole mu tabo shi. Ka san ba za ka haifi yaro ka bar shi ya je ya yi ta gaririya ya yi ta wasa da yaran mutane ba, ai ka kan yi wasa da danka. To ka ji dalilin da yasa nake yawan tabo Yakubu Lere.
Ba gaba bace kenan karma yadda wasu ke tsammani?
A'a, ba wata gaba tsakaninmu, sai zaman lafiya ma.
Akwai Alh. Aliyu shehu Hadeja, Wada Aliyu Gudufa, Baba Yaro, Ali Kwara da sauransu, mecece alakarka da su?
Wadannan mutane, ka san duk abinda za ka yi, ya kamata a ce kana da iyayen gida wadanda kake ji da su. Saboda idan ka kula da yadda kasar nan take, sai kana da wani jigo sannan ka yi wandaka a kasar nan. To wadannan sune jigogina. Kuma duk wani abu na Allah ya kiyaye ko na farin ciki sune. Amma ai baka sanya Yariman Bakura ba.
Ai na yi tambaya ne akan wadanda jama'a suka ji kana yawan ambatonsu.
To shi ma Yariman Bakuran kwanan nan za ka ji ina yawan ambatonsa.
Shi kuma menene tsakaninku da shi?
Shi ma zaman lafiya da mutunci, da kuma Perm Sec. na jihar Katsina wato Habu Danmallam da Alh. Tasi'u Mashi duk za ka ji ina yawan ambatonsu, saboda duk wadannan jigogina ne wadanda ko ina na je ina ji da su.
An kawo shari'ar Musulunci a jihar Kano, amma sai ta fi zafi akan 'yan fim, me kake ganin ya kawo hakan?
Ka san gaskiya akwai abinda har yanzu malamai basu gane ba game da wannan sana'a. Kullum idan za ka haifi yaro ka yi ta la'antarsa, ba zai taba yi maka daidai ba. Dole ne sai ka samu mai yi maka gyara a al'amurranka. To amma Alhamdulillahi, duk da dai ana gudunmu, mun hadu da hukuma ta gari mai kula da hakkin kowa. Ka ga idan ka kula, wannan gwamnatin ta Mallam Shekarau ta san abinda take yi. Domin shi Malam Ibrahim Shekarau ya fuskanci cewa su 'yan fim din nan malamai ne, saboda yadda za a tsaya a sauraremu, ba za a tsaya a saurari wa'azi ba.
To amma idan malaman suka jawo mu jikinsu kamar yadda shi gwamna ke nufin yi yanzu, ka ga kenan idan aka rubuta labari, ba za a yi shi ba sai an samu malam an ce mashi ga labari kaza in akwai gyara a gyara, idan kuma batun sanya musulunci ne a ciki duk za mu yi. To amma idan kullum za ka yi ta la'antar mutum, to sai ma ya ce bari ma ya yi ya ga ya za ka yi da shi, domin ba wanda ya isa ya kashe wani sai kwanansa ya kare.
Ku 'yan fim ana yawan ce maku ku 'yan iska ne, kare kanka.
Duk wanda ya cewa dan fim dan iska, to shine dan iskan, ko kuma in ce ba shine dan iskan ba, tsohonsa ne dan iskan, ni dai abinda na ajiye kenan. Ni in ba wasa nake yi ba, idan ka zo ka kalleni baka isa ka ce mani dan wasan kwaikwayo ne ba. Saboda haka duk wanda ya ce mani dan iska, ba ni ya ce mawa ba, tsohonsa ne dan iska, hasalima, ni malami ne.
Amma ka yarda a cikinku akwai masu zubar da mutuncin 'yan wasa?
Na yarda da wannan, amma abinda ke damun mu mu 'yan wasa, gaskiya bamu da hadin kai, kuma kullum hassada itace a cikin ran mu, muna son mu ga bayan wane ko wance. Ko kuma idan aka ce wane ya yi bako, kullum burin mutum kada ya hada ka da shi, sai ya tare shi, a nan ya samu abinda ya zo maka da shi, ya je ya shirya maka karya, wanda bai fi ya baka naira dubu ko dari biyar ba. Ka ga duk irin wannan muguntar muna yiwa junanmu, musamman ma mu da yake ba cikin birni muke ba, a kauye muke, an fi yi mana irin wannan 'yar dakilen. Domin wasu abubuwan ma sai an yi sannan mu ji.
Ka ga misali, akwai abinda aka yi a gidan gwamnatin nan wanda ya bada kyaututtuka, ka ga wannan ma mu da muke kauye ba a sanar da mu ba, sai dai kawai muka ji an yi. Kuma ko da mutum ne yake son ya zo wajenmu, idan ya dira a hannun 'yan Sentimental, sai sun san ya za a yi a hana shi zuwa wajen mu, saboda mugunta. Amma kuma akwai mutanen da ba 'yan wasan kwaikwayo ba, su suke ja mana zagi.
Misali, na taba zuwa birnin Kano, sai na ga wani tsoho, ban ma taba ganinsa ba, amma akwai Kaset a hannunsa yana yawo da Mota yana rabawa 'yanmata, kowacce ya ba kaset din wai za ta yi Mamin, sai ya lalatata, sannan kuma mu yake jawowa zagi, kuma ba dan fim bane. Irin wadannan mutanen duk muna tare da su. To amma idan da 'yan wasan kwaikwayo suna da hadin kai, muma ba a isa a shigo a taka mu ba.
Shin wai cikin 'yan Sentimental din nan, akwai wanda wasan shi yake baka sha'awa?
Sosai ma.
Kamar wa kenan?
Am, akwai wannan Gayen da yake tashe yanzu, wa ma sunanshi?
Sani Danja?
Ni ina ruwana da wannan Karas din, abokin wasana ne wannan yaron.
Nakwango?
A'a, dan Jos din nan.
Wato Aminu Almah?
Ba Almah ba, Adamu Usher, ka ga wannan, yana bani sha'awa.
Me yake burgeka game da shi?
Ni ka san abinda yasa jinina bai hadu da 'yan Sentimental ba, wai sun san wannan dan wasa ne, amma sai su rika nuna masa girman kai, kuma ka san abokin sana'arka ne, amma sai ka rika yi masa girman kai. To Adamu Usher ba shi da girman kai, kuma duk inda ya ji wani abu na Allah ya kiyaye, ya kan zo ya yi jaje, kuma a yi da shi. Musamman akwai wani karatu da na yi tsakaninmu da 'yan Sentimental game da rasuwar Kulu da Yautai. Ka ga akwai mutanen da tun daga farkon rasuwar har zuwa sadakarsu duk tare muka yi, kuma wai ma wadanda ba mu zata ba.
To ka bamu sunayen wadannan mutanen mana, tunda abin alheri suka yi.
Akwai Adamu Usher, Abba El-Mustapha, Ibrahim Mandawari, Shehu Kano, Ishaq Sidi Ishaq, Akwai wadanda dai suna nan na rike a zuciyata, wadanda basu zo mana ta'aziyya ba, sai dai idan mun hadu da su sai su ce wai Allah ya kiyaye. Ka ga misali, tsakanina da Allah babu wani abu a tsakanina da su Sani Danja da su Ali Nuhu, amma mutanen nan na ajiye su a zuciyata. Kuma na fada masu idan ma su ba za su mutu ba, to ai wasu 'yan uwansu za su mutu. Mu ma ba za mu je masu ta'aziyya ba.
To a mata kuma wacece take burge ka?
Ai ni a mata babu wadda take burgeni irin Daso.
'Yan mata fa?
'Yan mata sai wannan Karas din, Safiya Musa.
Me yasa Daso take burge ka?
Abinda yasa take burge ni, Daso mace ce mai sanin mutuncin dan wasa. Kuma takan ziyarce ka bata ma sanar da kai ba. Ko bana nan Daso takan zo gidana ta ce zuwa ta yi ta gaisa da iyalina. Ni dai a 'yan wasan kwaikwayo mata babu yadda zan fassara Daso.
Ita kuma Safiya Musa fa?
Dama kamar yadda na fada a baya, bana son dan wasa mai girman kai. In ma za ka yi girman kai, to ka yiwa wanda ba sana'arku daya ba. Amma sana'arku daya, sai mutum ya zo ya yi wani sharbebe da lebe ko kuma ya yi wani dukunkum da shi. Kai in shafe shafen nan ne muma mun iya shi, amma saboda mu bamu yi, ko kuma don bamu shige da fice ne, shine wai sai ka ga dan wasa ka daga masa kai, ka kuma nuna ba sana'ar ku daya ba.
Yanzu ka yi finafinai sun fi dubu, ka bamu guda uku da ka fi ji da su.
Akwai Kauran Mata, Kowa Ya Debo Da Zafi, da kuma Mai Dawa.
To Jahilci Ya Fi Hauka fa?
Wannan ni baya gaba na.
To saboda me, saboda ka sha zagi wajen malamai koko?
Ai wannan ma yana daya daga cikin Kaset din da zan gode mawa, domin duk abinda ka yi aka zage ka ya fi dago ka.
Kana da makiya da yawa, me za ka ce masu?
Sai godiya, su ci gaba kar su fasa.
Su ci gaba da kin ka?
Eh,
To masoyanka fa?
Su ma su cigaba kar su fasa.
Wane irin yanayi ka fi so, sanyi ko zafi Rani ko kuma Damina?
To ai ba wanda yake son takura. Ita duniya Allah ya halicce ta ne, dole ne a yi sanyi, dole ne a yi zafi, dole ne a yi Damina dole kuma a yi Rani. Kuma kamar yadda nake fada, akwai wasu daga baya za ka ga sun bugo waya wai suna cewa to su wane da wane dai sun mutu saura kai. Ka ga ya nuna cewa yana murna kenan an mutu. Ina kira ga mutane kowa ya je gida ya zauna ya yi shiru, ina tabbatar masa da cewa yana nan zaune a gidan zai ji an ce Salamu alaikum, kuma yana gidan zai ji an ce Allah ya kiyaye. To haka mutuwa take. Har in ka san za a haihu, to za a fa mutu. Haka zalika in ka san za a ce maka sannu da zuwa, to wata rana za a ce maka sauka lafiya.
To mu koma akan tambayar da na yi maka ta irin yanayin da ka fi so.
Ni da yake dan kauye ne na fi son Damina saboda noma.
Wane irin abinci ka fi so?
Ni dama abincina Dawa.
Dawar wace iri, ai ana tuwo da ita ko Kunu?
Abincina wanda na fi so Dawa da Gero saboda Koko tunda mu 'yan kauye bamu san shayi ba.
Dawa fa?
Dawa saboda a yi tuwo miyar kuka mu ci mu koshi, mu ji jikinmu ya yi kwari, ba ka zo ba a dan tunkudeka ka zube.
Sutura fa?
Na fi son yadi wanda zan shekara da shi ina gurzawa, ba in sa Shadda ba kwana biyu in ga tana kodewa.
Wace kasa ka fi son ka je a duniya?
A kasashen waje, ka san mu 'yan kauye kanmu a duhu yake, amma muma muna sha'awar mu ganmu a wajen. Kuma ni dai a raina, ina sha'awar zuwa Ghana saboda Alh. Attah. Kuma duk burin Musulmi, ya ga ya je ya ziyarci dakin Allah.
Yanzu Ghana da ka ce kana son zuwa, me yasa kake son zuwa can? Ka san an ce "Shimfidar Fuska, Ta Fi Shimfidar Tabarma". Ka san ko mutum bai baka ko sisi, baka san mutum ba ya karbeka hannu biyu-biyu har ka bar garin lafiya, babu abinda za ka ce masa.
Wace kyauta aka taba yi maka wadda ba za ka taba mantawa da iata ba?
Ta kai wajen hudu. Ka ga Baba Yaro ya bani kyautar Mota. Bashir Zubairu, shugaban Majalisar dokoki ta jihar Kaduna ya bani Mota. Danmalam shima ya bani kyautar Mota. Sai kuma kankat, Yarima ya bani kyautar Mota.
An taba baka sarauta?
Eh, an taba bani a Das, kuma har yanzu ina tare da ita.
Ga shi kana da sarauta, amma ban ganka da fadawa ba, hasali ma, sai na ganka a kyamushe, kuma a tube?
Nan ai a Wudil nake, kuma ni sarauta ta a Das take, can kasar Bauchi. Amma idan a gobe na je can Das, to zan sa Rawani kuma babu sauran wasa sai mazurai har sai na dawo nan Wudil.
An ce an dakatar da kai daga yin hawa a Kano, da gaske ne?
Ba a dakatar da ni ba, sai dai an yi kamar Sallah biyu ban yi ba. Da karamar Sallah ka san kowa yana dan karime-karimen abinci, wannan ne ya janyo ban yi hawa ba. Sannan kuma babbar Sallah ina Umrah. Wannan shine dalilin rashin hawa na. Kuma har gobe idan Sallah ta zo, sai an san ya za a yi a yi hawa da ni. Amma akwai wani hawa da ban yi ba saboda na je Zariya an yi da ni.
To me ya kai ka Zariya, saboda ta fi Kano ko ya abin yake?
Ka san shi Sarkin Kano, Sarkin Musulunci mai adalci ne. Kullum abinda yake fada mana shine, mu rika bazuwa inda kansu bai waye ba, mu rika wayar masu da kai. Idan ka kula a Zariya sukuwar da na yi, wani bai isa ya yi ta ba a Zariyar.
Ka ce ka ji dadi akan wasu abubuwa da aka yi maka, sannan a rayuwa akwai bakin ciki da farin ciki. Wane abu ne wanda ya taba samunka na bakin ciki sanadiyyar wannan sana'ar da ba za ka taba mantawa da shi ba?
Ni abinda yake bata mani rai kawai a wannan sana'a bai wuce rashin hadin kan 'yan wasa ba.
Ya kake ganin za a yi a samu hadin kan?
Ai mu 'yan daukar gara ne. Idan suka hada kai to muna tare.
Idan aka nemi hadin kanka a shirye kake kenan?
Ko da yaushe kuwa. Kuma ina kira ga 'yan wasa. Wannan sa mu a gaban da aka yi ana son a ga bayan mu, mutum ya daina jin tsoro. Mutum dai kawai ya bi iyayensa, domin duk wanda ya bi iyayensa, to ko uban waye zai yi ya bar ka. Ni kuwa na gode Allah, domin kuwa bana son abinda ran iyayena zai baci a kai. Don haka idan na fito bana tsoro kuma bana shayi, duk fitowa sai sun ce a dawo lafiya. Don haka babu abinda ke bata mani rai, tunda ran iyayena bai baci ba.
Tambaya ta karshe, da za ka mutu ka dawo, za ka sake yin wasan kwaikwayo, ma'ana, ka taba yin da na sanin shiga harkar fim?
Ban yi ba, sai dai godiya. Ai mu yanzu sai dai rokon Allah muke yi, don Allah ya dada buda mana akan wannan sana'a ta wasan kwaikwayo.
To mun gode Ibro.
Ni ma na gode

No comments: