Friday, January 18, 2008

An kori Jaruman Hausa 23 daga Industry

Gaskiyar Nura Hussain da yake cewa wannan abu da ya faru, masifa ce da za ta iya shafar kowa da kowa. To yayin da babu shakka muka yarda da shi akan wannan, ta wani bangaren kuma za mu iya cewa Allah ya yi amfani da ita Maryam din ce domin ya kawo gyara a Industiri. Dama kullum abinda ya kamata Mumini ya rika yin addui'a akai shine, kada Allah ya yi amfani da shi ya zama ishara ga wasu.

An dade ana kuka dangane da tabarbarewar tarbiyyar 'yan fim musamman ma mata, amma shugabanni sun yi kunnen uwar shegu da wadannan koke-koke da jama'a suke yi. Al'amarin da ya kai ma badala ake yi a bayyane, ba sa ko jin tsoron bakin jama'a. Sai ka gayyaci 'yar wasa, amma har karfe biyu ba ta tashi barci ba, balle ta fito aiki. Yayin da furodusoshi suke tsiyacewa suna taka Sayyada, su 'yan matan dada kazancewa suke yi da kudi suna sayen manyan motoci, kuma kowa ya san cewa ba a harkar suke samun kudaden da suke sayen motocin ba. Amma aka rasa wanda zai yi masu magana.

Sau da yawa an sha tsintar fitattun jarumai a buge, yashe a gefen titi, amma in ka yi magana sai a ce ka rufa asiri. Hatta kwanan nan da wata jarumar ta shawo, ta tube tsirara, shugabanni ba su zartar da wani hukunci akanta ba. 'Yan matan sun zama manyan karuwai, ana ji ana gani an kasa tsawata masu. Da yawa daga cikin manya kuma da ya kamata su tsawata, sune kuma Kawalai. Don haka sai harka ta yi matukar lalacewa, babu babba ba yaro.

A sakamakon bayyanar wannan hoton na Hiyana, yasa shugabannin Indusatiri suka gudanar da taron gaugawa, inda aka yanke hukuncin korar jarumai goma sha takwas. Sha shida mata, biyu maza. Da muke zantawa da shi ta wayar tarho, shugaban 'yan wasan jihar Kano, Alhaji Sa'idu Gwanja ya ce, an dauki wannan matakin ne domin dawowa da harkar martabarta. Ya ce wadanda aka koran, ana da tabbacin irin munanan halain da suke aikatawa ne, wadanda suke zubarwa da sana'ar mutunci a idanun jama'a.

Ya kara da cewa, akwai wadanda aka kora saboda zargin karuwanci da shaye-shaye. Da kuma wasu da aka lura suna Kawalci. Sai kuma Kubura Dhacko da Muhibbat Abdus-Salam, wadanda aka kora saboda su ne suka yayata hotunan Hiyana. Sa'idu Gwanja ya kara da cewa, tun daga ranar sha biyu ga watan nan, an dakatar da shirin fim a Arewa gaba daya har sai yadda hali ya yi.

Haka kuma a cewarshi, an kafa wani Kwamiti mai mutum goma sha takwas a karkashin shugabancin Ibrahim Mandawari, wanda zai yiwa harkar fim garanbawul gaba daya. Daga nan sai shugaban ya yi kira ga jama'a da su taimaki 'yan fim da addu'a da shawarwarin yadda za a inganta sana'ar fim. Wadanda aka kora din dai, an tabbatar da laifuffukan da suka shafi Karuwanci, Shaye-shaye, Kawalci, Rikici akan samari da kuma tara mata. Yanzu dai ga sunayen jaruman da aka kora har abada daga Industiri.

No comments: